Home Labaru Kiwon Lafiya Hadarin Mota: Mutane 19 Sun Hallaka, 7 Sun Jikkata A Jihar Kano

Hadarin Mota: Mutane 19 Sun Hallaka, 7 Sun Jikkata A Jihar Kano

835
0

Mutane 19 sun rasa rayukan su, yayin da kimanin 7 su ka jikkata a wani mumunan hadarin mota da ya faru a garin Dinyar Madiga kusa da karamar hukumar Takai a jihar Kano.

Hadarin dai ya faru ne da yammacin ranar Lahadin da ta gabata, inda motoci hudu su ka ci karo da juna yayin da su ke kokarin kauce wa ramukan da su ka cika hanyar.

Kwamandan hukumar kiyaye hadura ta kasa na yankin Zubairu Mato ya bayyana wa manema labarai cewa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 6 na yamma.

Ya ce hadarin ya shafi motoci hudu mallakar gwamnatin jihar Kano, kuma wadanda su ka rasa rayukan su su hada da maza 14 mata 3, da kananan yara 2.

Mato ya bayyana faruwar hadarin da gangancin direbobi wajen gudu da kuma rashin kyawun hanya, ya na mai kira ga direbobi su rika bin dokar tuki domin kiyaye hadurra da asarar rayuka.