An bayyana hanyoyi 22 da gwamnatin tarayya za ta iya samun kudaden shiga, wadanda za su iya maye gurbin kudaden da ake samu ta hanyar cinikin danyen mai a kasuwannin hada-hada ta duniya, kamar yadda shugaban Hukumar Karfafa Kayan Kasuwannin ketare Segun Awolowo ya bayyana.
Awolowo ya bayyana wa manema labarai haka ne, jim kadan bayan kammala ganawar da ya yi da Shugaba Muhammadu Buhari a fadar sa da ke Abuja.
Ya ce ya fayyace wa Shugaba Buhari hanyoyin da za a bi domin fadada tattalin arzikin Nijeriya ta hanyar kara samun kudaden shiga, ya na mai cewa duk abin da ya shaida wa shugaban kasa ya na cikin tsarin da kwamitin fadada tattalin arziki da Majalisar Inganta Tattalin Arziki ta Kasa ta kafa.
An da kafa kwamitin musamman ne a karkashin shugabancin gwamnan Jihar Jigawa Abubakar Badaru, inda aka dora masu nauyi da lahakin lalubo sabbin hanyoyin samun kudaden shiga.
Daga cikin hanyoyin da Awolowo ya bayyana, akwai shirin da Babbban Bankin Nijeriya ke yi na bada lamuni ga manoman da za su rika noma kayan amfanin gona masu kawo ribar kasuwanci, irin su Cocoa da Yazawa da Tumatir da sauran su.