Home Labaru Gwamna Masari Ya Bukaci Gwamnoni Su Yi Sulhu Da ‘Yan Ta’adda

Gwamna Masari Ya Bukaci Gwamnoni Su Yi Sulhu Da ‘Yan Ta’adda

203
0
Aminu Bello Masari, Gwamnan Jihar Katsina
Aminu Bello Masari, Gwamnan Jihar Katsina

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya yi kira ga takwarorin shi na sauran jihohin arewa maso yammacin Nijeriya su yi sulhu da ‘yan ta’adda.

Da ya ke jawabi jim kadan bayan kammala wata ganawa a kan tsaro, Masari ya ce gwamnatin shi ce ta fara kawo tsarin yin sulhu da ‘yan ta’adda, don haka ya bukaci a yi wa ‘yan ta’addan afuwa.

Ya ce dole ne jihohin Kaduna da Neja da Zamfara da Kebbi da dai sauran su su zauna su yi sulhu domin a samu abin da ake bukata.

Gwamna Masari ya bayyana cewa, an fara wani aikin samar da tsaro na musamman domin maido da zaman lafiya a kananan hukumomi 8 da ke fama da matsalar ta’addanci a jihar Katsina.