Home Labaru Kiwon Lafiya Covid-19: An Tsawaita Dokar Hana Fita A Ekiti

Covid-19: An Tsawaita Dokar Hana Fita A Ekiti

264
0
Yadda jami'an tsaro suka sanya wasu masu karya dokar hana fita gwale-gwale
Jami'an tsaro na kallon wasu masu karya dokar hana fita suna gwale-gwale a jihar Ekiti

Gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi ya kara wa’adin dokar hana fita da mako 2 domin takaita yaduwar cutar Coronavirus a jihar.

Gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi

Fayemi ya bayyaba haka ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Biodun Oyebanji ya sa hannu a ranar litinin din da ta gabata.

Sai dai ya ce za a kyale mutane su gudanar da harkokinsu na yau da kullum daga karfe 6 na safe zuwa 2  na rana, domin su samu damar sayen kayan abinci a kasuwa. 

Haka kuma, daga ranar Talatar nan tilas ne kowa ya rika amfani da abin rufe fuska, domin rage yaduwar cutar a jihar, tare da cewa za a samar da takunkumin rufe fuska ga ma’aikatan da aka ba damar fita zuwa wajen aiki.

Gwamana Fayemi ya ce, gwamnatin sa za ta ci gaba da koyar da daliban makarantun firamare da sakandare a kafar yanar gizo, saboda dabbaka dokar hana cinkoson mutane a waje guda.