Home Labaru Gwamnatin Tarayya Ta Ce A Hau Jirgin Kasa Kyauta Tsawon Mako 1...

Gwamnatin Tarayya Ta Ce A Hau Jirgin Kasa Kyauta Tsawon Mako 1 Albarkacin Kirsimati

31
0

A ranar juma’ar nan 24 ga watan Disamba ne gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za a hau jirgin kasa kyauta a duk fadin Najeriya na tsawon mako daya albarkacin bukukuwan Kirsimati da na sabuwar shekara.

Gwamnatin t ace za a fara cin gajiyar tagomashin ne daga ranar Juma’a, 24 ga watan Disamban 2021 zuwa ranar hudu ga watan Janairun 2022, kamar yadda Kakakin Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC), Mahmoud Yakubu ya tabbatar a cikin wata sanarwa.

Ya ce garabasar za ta shafi dukkan sassan jiragen kasa da hukumar ke gudanar da su.

Hanyoyin da garabasar za ta shafa sun hada da Abuja zuwa Kaduna da Legas zuwa Ibadan da Warri zuwa Itakpe da Kano zuwa Legas da Minna zuwa Kaduna da kuma Aba zuwa Fatakwal.

Shi ma Shugaban hukumar ta NRC, Injiniya Fidet Okhiria, ya ce, an yanke shawarar yin garabasar ne da hadin gwiwar Ma’aikatar Sufuri don saukaka wa jama’a wahalhalun da suke fuskanta yayin tafiye-tafiye lokacin bukukuwan Kirsimati.