Home Labaru Gwamnoni Na Iya Ƙoƙarinsu Wurin Samar Da Tsaro A Jihohinsu: Kayode Fayemi

Gwamnoni Na Iya Ƙoƙarinsu Wurin Samar Da Tsaro A Jihohinsu: Kayode Fayemi

149
0

Shugaban ƙungiyar gwamnonin Nijeriya kuma gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi ya ce, yanayin da Nijeriya ke ciki musamman ta bangaren tsaro abin damuwa ne ga ‘yan ƙasar baki ɗaya.

Gwamnan, ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai, inda ya ce matsalar tsaron da ake fama da ita tana mayar musu da hannun agogo baya ta ɓangaren ayyukan da suke yi wa al’umma.

Ya ce, sau da dama ayyukan da aka tsara za a yi kan wargaje sakamakon hare-haren da ake kaiwa, yana mai cewa suna ɗaukar matakai daban-daban domin magance matsalar tsaro ta hanyar haɗa gwiwa da gwamnatin tarayya da al’ummomi.

Gwamnan ya kara da cewa, suna iya bakin kokarinsu don ganin an kawo karshen matsalar, amma akwai iyakar da ba su da ikon ketarawa saboda ba su da iko da jami’an tsaro duk da cewa ana kiran su da manyan jami’an tsaron jihohinsu.

A cewarsa, matuƙar ‘yan bindiga suka ci-gaba da kai wa ‘yan Nijeriya hari, wannan na nuna cewa da sauran aiki, har sai lokacin da aka daƙile miyagun laifuka a fadin ƙasar.