Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za ta ƙaddamar da riga-kafin korona zagaye na uku a ranar Juma’a mai zuwa.
Jaridar Punch ta ruwaito daraktan lafiya a matakin farko na ƙasa, Dakta Faisal Shuaib na sanar da hakan yayin ƙaddamar da riga-kafin a sansanin ƴan gudun hijira dake Abuja.
Shuaib ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta yanke shawarar amfani da rigakafin korona na Kamfanin Pfizer Bio-N-tech a zagaye na ukun.
Tuni dai wasu ƙasashen duniya suka soma riga-kafin zagaye na uku domin ƙara ƙarfin riga-kafin a jikin waɗanda aka yi wa zagayen farko da na biyu.
You must log in to post a comment.