Home Labaru An Tsinci Gawar Kwamishinan Kimiyya Da Fasaha Na Katsina

An Tsinci Gawar Kwamishinan Kimiyya Da Fasaha Na Katsina

44
0

Wasu da ba san ko su wane ne ba sun yi wa Kwamishinan Kimiyya da Fasaha na Jihar Katsina, Dokta Rabe Nasir, kisan gilla.

Maharan sun bude wa kwamishinan wuta ne a gidansa da ke Rukunin Gidajen Fatima Shema a garin Katsina da yammacin ranar Alhamis.

Bayanai sunce “An harbe marigayi Dokta Rabe Nasir ne bayan Sallar La’asar a gidansa da ke Rukunin Gidajen Fatima Shema.

Kafin zamansa kwamishinan, marigayin Dokta Rabe shi ne Mashawarcin Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina a kan Kimiyya da Fasaha.

Dokta Rabe Nasir haifaffen garin Mani ne a Karamar Hukumar Mani ta jihar Katsina kuma an haife shi ne a watan Oktoban shekarar 1960.