Shugaba Muhammadu Buhari ya bada tabbacin gudanar da cikakken bincike kan mutuwar wani ɗalibi a jihar Legas.
Ana zargin Sylvester Oromoni mai shekaru 12 ya mutu ne bayan azabtar da shi a dakin kwanan ɗaliba na Kwalejin Dowen da ke Legas a watan da ya gabata.
A wata sanarwar da fadarsa ta fitar a ranar Alhamis, Buhari ya yi Allah wadai da Al’amarin, tare da alƙawalin cewa zai kasance sanadin kawo ƙarshen matsalar kungiyar asiri da kuma cin zarafin ɗalibai a makarantu.
A yayin ziyarar aiki da ya kai yau a birnin Legas, Shugaban ya ƙaddamar da wasu ayyuka, ciki har da ƙaddamar da wani littafi wanda Chief Bisi Akande ya rubuta.
You must log in to post a comment.