Home Labaru Gwamnatin Tarayya Ta Gabatar Da Binciken Da Ta Gudanar

Gwamnatin Tarayya Ta Gabatar Da Binciken Da Ta Gudanar

16
0

Gwamnatin tarayya ta gabatar da binciken da ta gudanar a kan ayyukan ta’addancin da ‘yan kungiyar a-waren ta IPOB su ka yi a fadin Nijeriya.

Ta ce ya zuwa yanzu, ‘yan ta’addan sun kai hare-hare a kan ofishohin ‘yan sanda 164 tare da babbaka wasu.

Ministan Shari’a Abubakar Malami ya bayyana haka, inda ya ce hare-haren ‘yan ta’addan sun kuma kashe jami’an ‘yan sanda 175.

Gwamnatin ta kara da cewa, ‘yan kungiyar IPOB sun kai hare-hare a kan ofishohin hukumar zabe ta kasa guda 19, sannan sun kona motocin hukumar guda 18.

Abubakar Malami, ya ce za’a dora alhakin duk wadannan ayyukan a kan shugaban kungiyar Nnamdi Kanu.