Home Labaru Ganduje Ya Kaddamar Da Dakarun Hisbah 5000 A Kano

Ganduje Ya Kaddamar Da Dakarun Hisbah 5000 A Kano

14
0

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya halarci bikin makon Hisbah da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata.

Ganduje ya Kaddamar da dakarun Hisbah na musanman har dubu 5 da 700, a karkashin Jagorancin Shugaban Hukumar Hisbah na Jihar Kano Ustaz Muhammad Ibn Sina.

Yayin taron, Ganduje ya kuma sauya wa jami’an Hisbah Kayan Sarki, da kuma karin girma ga dukkan jami’an da su ka kwashe tsawon shekaru shida su na aiki.

Gwamna Ganduje, ya kuma yaba da yadda ‘yan Hisba su ke gudanar da aikin su, inda ya ce za a duba yiyuwar kara masu albashi.