Home Labaru EFCC Ta Tsare Tsohon Shugaba Majalisar Dattawa

EFCC Ta Tsare Tsohon Shugaba Majalisar Dattawa

8
0

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, ta fara yi wa tsohon shugaban majalisar dattawa Anyim Pius Anyim tambayoyi bisa zargin almundahana tare da karkatar da dukiyar al’umma.

Sanata Anyim wanda ya isa helkwatar hukumar da ke unguwar Jabi a birnin Abuja, ya shafe sama da sa’o’i 6 ya na amsa tambayoyi, yayin da wasu rahotanni ke cewa ba a bar shi ya koma gida a ranar Lahadin da ta gabata ba.

Duk da ya ke babu wani cikakken bayani game da zarge-zargen da ake yi ma shi, wata majiya ta alakanta zuwan sa ofishin hukumar zargin almundahanar da ta shafi tsohuwar ministar sufurin jiragen sama Sanata Stella Oduah.

Majiyar ta ce, an gano wani bangare na kudaden gyaran da ya kamata a yi a bangaren sufuri a lokacin da ya kai Naira miliyan 780, wanda ake zargin an karkatar da su zuwa wani kamfani da Sanata Anyim ke matsayin darakta a ciki.

Tsare Sanata Anyim dai ya na zuwa ne, kwanaki kadan bayan an ambaci sunan sanata Stella Oduah a cikin badakalar takardun Pandora a matsayin daya daga cikin ‘yan Nijeriya 10 da ke boye dukiyar su a wuraren da ake kin biyan haraji.