Gwamnatin tarayya, ta amince a jinginar da filin jirgin sama
na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, da na Mallam Aminu Kano
da ke Kano.
Amincewa da matakin dai ta zo ne, a wajen taron majalisar zartarwa ta kasa da aka gudanar a Abuja.
Ministan sufirin jiragen sama Hadi Sirika da sanar da manema labarai cewa, za a jinginar da filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe ne na tsawon shekaru 20, yayin da za a jinginar da na Mallam Aminu na tsawon shekaru 30.
Hadi Sirika, ya ce taron ya kuma amince da sauya wa ma’aikatar suna daga ma’aikatar kula da sufirin jiragen sama zuwa ma’aikatar kula da sufirin jiragen sama da sararrin samaniya.














































