Wani sabon rahoto ya nuna cewa, Niajeriya ta na bukatar
akalla Dala biliyan 12 domin gudanar da aikin tsaftace
malalar man fetur a jihar Bayelsa.
Rahoton ya bayyana manyan kamfanonin mai na Shell da Eni a matsayin wadanda su ka gurbata jihar Bayelsa, kuma za a dauki sama da shekaru 12 ana aikin tsaftace jihar.
Ma’aikatar Mai da Muhalli ta jihar Bayelsa ce ta tattara bayanai, bayan a shekara ta 2019 ta fara gudanar da bincike a kan tasirin malalar man fetur a jihar.
Haka kuma, Ma’aikatar ta nazarci wasu hujjoji da ta samu tare da gudanar da gwaje-gwajen jini a kan mutanen da ke rayuwa a yankunan da malalar man ta yi wa illa, inda ta gano cewa akwai guba mai yawa da tsiyayar man ta yadu a iska da ruwan sha har ma a cikin jinin al’umma.
Ma’aikatar ta ce akwai sakacin kamfanonin wajen samun wannan matsalar, domin sun gaza daukar matakan da su ka dace na kariya.
You must log in to post a comment.