Majalisar wakilai ta bukaci hukumar yaki da cin hanci da
rashawa EFCC ta gabatar mata rahoton duk mukaman da aka
bada a lokacin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.
Rahotanni sun ce, kwamitin kula da daidaito wajen ayyuka da albarkatun kasa na majalisar zai gudanar da bincike na musamman kan nade-nade tsohon shugaban kasar.
An tsaida matsayar ne, bayan d ‘yan majalisar sun amince da kudirin da dan majalisa Paul Nnamchi ya gabatar, inda ya ce akwai bukatar EFCC ta gudanar da aikin ta yadda doka ta tanada, domin hakan zai bada dama a yi wa kowane yanki adalci a rabon mukamai.
Dan majalisar ya kara da cewa, aikin hukumar EFCC ne ta sa ido kuma ta tabbatar ana bin dokar daidaito idan an tashi rabon mukamai da damarmaki.