Gwamnatin tarayya ta ce ta yi nasarar kwaso daukacin ‘yan
Nijeriya da suka makale a birnin Khartoum na kasar Sudan.
Sakataren dindindin na Ma’aikatar Jin-kai Dakta Sani Gwarzo ya bayyana haka, yayin da ya tarbi tawaga ta biyu mai kunshe da mutane 130 da ta isa filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja.
Rahotanni sun ce, mutanen sun iso ne da misalin karfe 3 da minti 10 na rana agogon Najeriya a ranar Juma’ar da ta gabata, wadanda su ka hada da maza biyu sauran kuma mata ne da kananan yara.
Dakta Sani Gwarzo ya ce sun yi nasarar kwaso kowa da kowa birnin Khartoum, ko da ya ke har yanzu akwai dimbin ‘yan Nijeriya da ke ci-gaba da kasancewa a kan iyakar kasar Masar.