Wata Kotu a jihar Jigawa, ta yanke wa tsohon Shugaban
jami’yyar APC na jihar Habibi Sara hukuncin dauri, bisa
zargin shirga kara da ya yi wa gwamnan jihar Muhammad
Badaru.
Kotun ta yanke hukunci ne, bayan ‘yan sanda sun kai kara gaban ta bisa zargin kantara wa gwamnan jihar karya.
Habibi Sara dai ya yi ikirarin cewa, gwamna Badaru da wasu manyan ‘yan siyasa sun zauna a kasar Saudiyya domin tattauna yadda za su yi wa gwamnatin zababben gwamnan jihar Umar Namadu Zagon kasa.
Ya ce Gwamnan ya sayi motoci domin raba wa kwamishinonin gwamnati mai jiran gado, inda ya ce hakan bai kamata ba domin ba aikin sa ba ne ya saya wa kwamishinonin sabuwar gwamnati motoci.
Sai dai a wata wasikar shigar da kara da ya aike wa ofishin ‘yan sanda, mai taimaka wa gwamnan ta fuskar yada labarai Habibi Muhammad, ya bukaci ‘yan sanda su kama Sara da wani mutum mai suna Karami Jahun, wanda ya ke zargin ya na yada labarin karya da kazafi a kan gwamna Badaru.
Mai shari’a Balago dai ya yanke hukuncin daure Habibi Sara a gidan yari har zuwa ranar 8 ga Mayu domin ci-gaba da sauraren shari’a.














































