Home Labaru Kiwon Lafiya Gwamnatin Legas Ta Hana Sallar Juma’a Da Taruwa A Coci Na Tsawon...

Gwamnatin Legas Ta Hana Sallar Juma’a Da Taruwa A Coci Na Tsawon Makonni 4

348
0
Gwamnatin Legas Ta Hana Sallar Juma’a Da Taruwa A Coci Na Tsawon Makonni 4
Gwamnatin Legas Ta Hana Sallar Juma’a Da Taruwa A Coci Na Tsawon Makonni 4

Gwamnatin jihar Legas ta a dakatar da gudanar da sallolin Juma’a da taron a coci-coci a wani mataki na yaki da yaduwar cutar Corona a jihar.

Kwamishinan harkokin cikin gida na jihar Anofiu Elegushi ya bayyana haka, inda ya ce gwamnatin ta hana duk wani taro da ya haura mutane 50 a fadin jihar.

Elegushi ya kara da cewa, gwamnatin jihar ta dauki wannan mataki ne bayan ganawa da shugabannin addinai, tare da cewa akwia bukatar mutane su rage cudanya da juna har sai barazanar annobar ta ragu.

Kwamishinan ya ce, wannan dakatarwar za ta shafe tsawon makonni hudu ana aiwatar da ita, haka kuma akwai yiwuwar sake duba umarnin bayan wani dan lokaci, sannan an kafa wani kwamiti da ya kunshi Musulmai da Kiristoci domin tabbatar da Masallatai da Coci coci sun bi wannan umarni.