Home Labaru Kiwon Lafiya Corona: NEMA Ta Bukaci A Hana Siye Da Siyar Da Kayan Gwanjo

Corona: NEMA Ta Bukaci A Hana Siye Da Siyar Da Kayan Gwanjo

769
0
Corona: NEMA Ta Bukaci A Hana Siye Da Siyar Da Kayan Gwanjo
Corona: NEMA Ta Bukaci A Hana Siye Da Siyar Da Kayan Gwanjo

Hukumar kula da bada agajin gaggawa ta kasa NEMA ta yi kira ga ‘yan Nijeriya su daina shigowa ko siyan kayan gwanjo domin gujewa kamuwa da cutar Corona.

NEMA ta bayyana haka ne a lokacin wani horarwa da shugaban cibiyar na yankin jihohin Imo da Abia Evans Ugoh ya shirya.

Ugoh ya kara da cewa, tamkar Nijeriya na ci gaba da gayyato cutar matukar aka ci gaba da shigowa tare da sayar da kayan.

Haka kuma, Evans Ugoh ya yi kira ga gwamnatin tarayya  a kan ta hana shigowa da kayan gwanjon cikin kasar nan, musamman ta hanyar hukunta duk wadanda aka kama da laifin yin hakan.

Leave a Reply