Home Labaru Kiwon Lafiya An Sake Samun Sababbin Masu Dauke Da Cutar Coronavirus A Kasar Saudi

An Sake Samun Sababbin Masu Dauke Da Cutar Coronavirus A Kasar Saudi

1137
0
An Sake Samun Sababbin Masu Dauke Da Cutar Coronavirus A Kasar Saudi
An Sake Samun Sababbin Masu Dauke Da Cutar Coronavirus A Kasar Saudi

Rahotanni daga Kasar Saudi Arabia sun tabbatar da karawar wadanda su ka kamu da cutar Corona a makon nan.

Saudiyya ta bayyana cewa mutane 67 sun kamu da cutar, lamarin da ya sa adadin masu dauke da cutar su ka karu.

Ma’aikatar lafiya ta kasar ta ce, daga cikin mutane 67 da su ka kamu da cutar, akwai 45 wadanda su ka ziyarci kasashen ketare a ‘yan kwanakin nan.

Bayanai daga kasar sun ce, mutanan sun samo cutar ne daga kasashen Ingila da Turkiyya da Sifen da Switzerland da Faransa da Indonesiya da kuma kasar Iraki.

Kawo yanzu an killace wadanda su ka kamu da cuta, sannan akwai mutane 19 da ke dauke da cutar a Riyadh, wasu 13 Jidda, yayin da ake Mutane 11 da ke jinya a Birnin Makkah.

Kawo yanzu dai, akwai mutane 23 da ake da labarin sun kamu da cuta a Gabashin kasar, Amma akwai mutane shida da su ka warke a halin yanzu bayan an killace su a asibiti.

Rahoton sun ce,  akwai akalla mutane 238 da su ke dauke da cutar Corona a kassahen Larabawa, wanda hakan ya sa  gwamnati ta dauki wasu tsauraran matakai.