Home Labaru Gwamnatin Katsina Ba Za Ta Sassautawa Wadanda Suka Kashe Hakimin ‘Yantumaki Ba

Gwamnatin Katsina Ba Za Ta Sassautawa Wadanda Suka Kashe Hakimin ‘Yantumaki Ba

602
0
Gwamnatin Katsina Ba Za Ta Sassautawa Wadanda Suka Kashe Hakimin ‘Yantumaki Ba
Gwamnatin Katsina Ba Za Ta Sassautawa Wadanda Suka Kashe Hakimin ‘Yantumaki Ba

Sakataren gwamnatin jihar Katsina Mustapha Inuwa ya ce kisar gillar da aka yi wa hakimin ‘Yan tumaki Abubakar Atiku ba zai sa gwamnatin jihar ta yi baya da yaki da ayyukan  ‘yan bindiga ba.

Direktan yada labaran sa, Abdullahi Inuwa ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, tare da cewa wadanda suka aikata wannan mummunan lamari da sauran masu aikata laifuka a jihar za su dandana kudar su.

Mustapaha Inuwa ya kuma bukaci al’ummar su ba gwamnati da hukumomin tsaro goyon baya, domin yaki da miyagun mutane ta hanyar taimaka musu da bayanai sirri da za su taimaka wajen magance matsalar.

Haka kuma, Inuwa ya nuna bakin cikin sa bisa kashe hakimin, sannan ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai son zaman lafiya da aiki tukuru, kuma ya bada gudunmawa wajen ganin an samu zaman lafiya a jihar.

Leave a Reply