Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Farfesa Umar Garba Danbatta a matsayin mataimakin shugaban hukumar sadarwa ta Nijeriya NCC.
Ministan sadarwa Isa Ali Pantami, ya mika bukatar kamar yadda dokar hukumar sadarwa ta shekata ta 2003 ta gindaya.
A cikin wata sanarwa da ministan ya wallafa a shafin sa na Twitter, ya ce shugaba Buhari ya amince da nadin ne a ranar Juma’a 5 ga watan Yunin shekata ta 2020, inda ya ce, an yi wannan nadin ne domin cimma manufa da tsare-tsaren tattalin arziki mai dogaro da fasahar zamani.
Ministan ya kuma yi kira ga Farfesa Umar Danbatta ya karfafa tare da inganta ma’aikatar da kuma tabbatar da tsare-tsaren gwamnatin tarayya ta hanyar da ta dace.
You must log in to post a comment.