Home Labaru Zulum Ya Mika Tallafi Ga Gidaje 10,000, A Garin Ran Da Ke...

Zulum Ya Mika Tallafi Ga Gidaje 10,000, A Garin Ran Da Ke Higar Borno

520
0
Zulum Ya Mika Tallafi Ga Gidaje 10,000, A Garin Ran Da Ke Higar Borno
Zulum Ya Mika Tallafi Ga Gidaje 10,000, A Garin Ran Da Ke Higar Borno

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya raba kayayyakin abinci da sauran kayayyakin masarufi ga gidaje dubu 10  a garin da ke Kala-Balge.

Wannan dai shine karo na hudu da gwamnan ke kai wa karamar hukumar tallafi domin saukakawa al’ummar saukin matsin rayuwa.

Jirgin dakarun sojin sama na Nijeriya ne ya dauki gwamnan daga Maiduguri zuwa garin Rann, sai dai a lokacin ziyarar, Zulum ya duba yadda ake raba kayan tallafin ga mata da kuma maza, tare da ‘yan Nijeriya 300 da ke jamhuriyar Kamaru.

Kowanne daga cikin mutanan ya samu buhun masara da katan din taliya da buhunan shinkafa biyu da kuma lita uku na man girki, sannan an karawa matan da turamen atamfofi.

Gwamna Zulum, ya jinjinawa ma’’aikatar jin kai hukumar cigaban yankin arewa maso gabas da kuma hukumar tallafin gaggawa tare da gidauniyar Dangote bisa irin taimakaon da su ke yi.