Home Labaru Dalilin Da Ya Sa Aka Tube Kaka Na Shekaru 100 Da Su...

Dalilin Da Ya Sa Aka Tube Kaka Na Shekaru 100 Da Su Ka Gabata – Sarkin Zazzau

31
0

Mai martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamali, ya ce an cire kakan sa daga kan karagar mulki shekaru 100 da su ka gabata ne saboda ya ki yin biyayya ga Turawan mulkin mallaka.

Da ya ke jawabi yayin bikin cikar shekarar sa ta farko a kan karagar mulki, sarkin ya ce ahlin sa sun shafe tsawon shekaru 100 su na jiran sarautar tun lokacin da aka cire kakan sa Aliyu Dan Sidi.

Ya ce an cire Aliyu Dan Sidi ne saboda ya ki yin biyayya ga Turawan mulkin mallaka tare da wani kakan sa, kuma wadanda su ka ziyarci Lokoja su ka kuma ga yanayin abubuwa sun zubar da hawaye saboda rashin adalcin da aka yi masu.

Mai martaba Sarkin Zazzau, ya ce Sarkin Gwandu Muhammadu Aliyu da Sarkin Kano Aliyu Na Sambo da Sarkin Zazzau Kwasau da Sarkin Zazzau Aliyu Dan Sidi da Sarkin Katsina Abubakar duk sun kasance a Lokoja, ya na mai fatan samun irin wannan karamcin, tare da addu’ar Allah ya saka masu da Gidan Aljanna.

Khalifa na Darikar Tijjaniya ta Nijeriya Muhammad Sanusi II, ya bukaci sarkin ya cigaba da hakuri tare da hada kan gidajen da sauran dangi domin samun nasara a mulkin sa.