Mai martaba Sarkin Argungun Alhaji Samaila Muhammadu Mera, ya nada Shugaban Majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan a matsayin Ganuwan Kabbi.
Daga cikin Wadanda aka yi wa nadin kuma akwai tsohon Gwamnan jihar Abia Orji Uzor Kalu a matsayin Kibiyan Kabbi, da Shugaban kamfanin raba wutar lantarki na jihar Kaduna Injiniya Garba Haruna Argungu.
Wadanda su ka halarci bikin sun hada da gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi, da Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, da Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari.
Daga cikin Sarakunan gargajiya kuwm akwai Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar Sa’ad III, Mai Martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, da Mai martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli.
You must log in to post a comment.