Home Labaru Gwamnatin Buhari Ta Fara Shirye-Shiryen Cefanar Da Asibitin Fadar Shugaban Kasa

Gwamnatin Buhari Ta Fara Shirye-Shiryen Cefanar Da Asibitin Fadar Shugaban Kasa

98
0

Fadar shugaban kasa ta hada-kai da ma’aikatar kudi da kasafi
domin a sa wasu kadarorin gwamnati a kasuwa.

Rahotanni sun ce, gwamnatin tarayya ta gano wasu hanyoyi guda uku da za a iya samun kudin shiga, wadanda su ka hada da wasu tsare-tsare da ayyukan da ake tunanin za a hada-kai da ‘yan kasuwa.

Babban sakataren gwamnatin tarayya na fadar shugaban kasa Tijjani Umar ya bayyana haka a Abuja, inda ya ce abubuwan da ake tunanin damka wa ‘yan kasuwa sun hada da sashen kula da gandun daji da gidan filin wasan yara.

Wata majiya ta tabbatar da cewa, akwai kuma batun babban asibitin fadar shugaban kasa da dakin shan magani da ake da su a garin Legas.

Leave a Reply