Home Labaru Samar Da Ayyukan Yi Baya Cikin Haƙƙokin Gwamnati – Adesina

Samar Da Ayyukan Yi Baya Cikin Haƙƙokin Gwamnati – Adesina

338
0

Mai ba kasa shawara ta fuskar yaɗa labarai Femi Adesina, ya
ce samar da ayyukan yi ga ‘yan ƙasa ba ya daga cikin
haƙƙoƙin da su ka rataya a wuyan gwamnati.

Adesina ya bayyana haka ne ta cikin shirin ‘The Morning Show’ na gidan talbijin na Arise Tv, lokacin da yake magana game da nasarorin da gwamnatin shugaba Buhari ta samu a cikin shekaru takwas da su ka gabata.

Ya ce abin da kawai gwamnati za ta yi shi ne samar da kyakkyawan yanayi ga kamfanoni masu zaman kan su don su samar da ayyuka, domin mafi yawan ayyukan da ake so ana samun su ne a kamfanoni masu zaman kan su.

Femi Adesina ya kara da cewa, gwamnatin shugaba Buhari ta cimma nasarori a ɓangarori da dama, wadanda su ka haɗa da ɓagaren mai da albarkatun iskar gas da ayyukan more rayuwa da samar da dokoki da tsaro.

Leave a Reply