Home Labaru ‘Yan Sandan Kasa Da Kasa Sun Gayyaci Kwamishinan Zaben Adamawa

‘Yan Sandan Kasa Da Kasa Sun Gayyaci Kwamishinan Zaben Adamawa

274
0

Rundunar ‘yan sanda ta ƙasa da ƙasa Interpol a Turance, ta
gayyaci dakataccen kwamishinan zaɓen na jihar Adamawa
Hudu Yunusa Ari, bisa tuhumar da ke kan sa game da abin da
ya aikata a lokacin ƙarasa zaɓen gwamnan jihar Adamawa.

Bayanin hakan, ya na kunshe ne a cikin wata wasiƙa da rundunar ta fitar, inda ta buƙaci Yunusa Ari ya bayyana a gaban ta domin amsa wasu tambayoyi a cibiyar hukumar tattara bayanai ta ƙasa da ke Abuja.

Sai dai takardar mai dauke da sa hannun Mataimakin shugaban ‘yan sandan Nijeriya mai kula da harkokin Interpol Garba Umar, ba ta bayyana ainihin ranar da kwamishinan zaɓen zai bayyana a gaban rundunar ba.

Idan dai ba a manta ba, Yunusa Ari ya ayyana Sanata A’isha Binani a matsayin wadda ta lashe zaben jihar Adamawa tun gabanin a kammala tattara sakamako, lamarin da ya saɓa wa tanadin kundin zaɓe na shekara ta 2022.

Wasu bayanai sun nuna cewa, bayan ayyana Binani a matsayin wadda ta lashe zaben, Yunusa Ari ya bar jihar Adamawa a wani jirgi kuma har yanzu babu wanda ya san takamaiman inda ya shiga.

Leave a Reply