Home Home Gwamnatin APC Ta Yaudari ‘Yan Nijeriya – Kwankwaso

Gwamnatin APC Ta Yaudari ‘Yan Nijeriya – Kwankwaso

36
0
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ziyarci birnin Abakalaiki na jihar Ebonyi domin yakin neman zabe.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ziyarci birnin Abakalaiki na jihar Ebonyi domin yakin neman zabe.

Kwankwaso, wanda ya samu rakiyar Injiniya Buba Galadima, ya kaddamar da ofishin yakin neman zaben jam’iyyar NNPP a kan babban titin Sabuwar Kasuwar Abakalaiki, daga bisani ya ziyarci gwamnan jihar Ebonyi David Umahi a masaukin shugaban kasa.

Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya ce shi da gwamna Umahi ba su ji dadin jam’iyyar PDP ba, shi ya sa su ka yanke shawarar barin ta saboda kura-kuran da ta ke tafkawa.

Ya ce NNPP ce jam’iyyar da za ta yi nasara a yankin Arewa, saboda Gwamnatin APC ta yaudari ‘yan Nijeriya.

Kwankwaso ya cigaba da cewa, abin da Nijeirya ke bukata shi ne wanda ya cancanta, kwararre, kuma mai rikon amana da kuma karfin da zai iya kai al’ummar kasar nan tudun mun tsira.