
Rahotanni na cewa, an kashe akalla mutane 28 a karamar hukumar Ado ta jihar Benue mai iyaka da jihar Ebonyi, sakamakon wani rikicin kabilanci tsakanin al’ummomin jihohin biyu.
Mazauna yankin sun ce, akasarin wadanda aka kashe mata ne da kananan yara, bayan an sake fardado dadaddiyar takun-tsakar da ke tsakanin kabilun jihohin biyu.
Shugaban Karamar Hukumar Ado James Oche ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Makurdi, inda ya ce rikicin ya barke ne sakamakon lalata wani wurin ibadar gargajiya na al’ummar Ebonyi.
Ya ce rikicin ya barke ne lokacin da wasu gungun mutane da lalata wurin ibadar gargajiyar a Ebonyi ya yi wa zafi su ka dauki doka a hannu, inda su ka afka wa al’ummar kauyen Ezza a jihar Benue.
Mista Oche, ya ce rikilcin ya yi sanadiyyar lalacewar kasuwa mafi girma a Ezza gaba daya, inda yanzu haka jami’an tsaro ke sintiri domin tabbatar da kawo karshen lamarin.
You must log in to post a comment.