Home Ilimi Gwamnati Ta Umarci Makarantu Su Fara Amfani Da Tsarin Ƙara Wa Malamai...

Gwamnati Ta Umarci Makarantu Su Fara Amfani Da Tsarin Ƙara Wa Malamai Shekarun Ritaya

93
0

Gwamnatin tarayya, ta jaddada amincewar da ta yi na fara amfani da Sabon Tsarin Shekarun Ritayar Malamai.

A Cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya Andrew Adejo, ya ce babu wata iyakar yawan shekaru da aka killace a kan batun ritayar malamai dangane da yawan shekaru a duniya ko yawan daɗewa su na koyarwa.

Sanarwar, ta kuma umarci waɗanda ba su son ƙara daɗewa su na aikin koyarwa su rubuta wasiƙar sanarwar ritayar su kamar yadda ake yi bisa ƙa’ida.

Dokar Tsarin Ritaya ta shekara ta 2022 ce ta ƙara wa malaman yawan shekaru su na koyarwa, wadda Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu..

Haka kuma, Dokar ta ce duk jami’an ilmi zai kasance shekaru 65 ne lokacin ritayar su, ko kuma shekaru 40 malami ya na aiki sai ya yi ritaya haka nan.

Ya ce yanzu ba a keɓance wasu an ce ba za a ƙara masu tsawon lokacin yin ritayar ba, amma duk wanda ke son yin ritaya sai ya rubuta ya sanar.