Home Labarai Kogi: Ana Binciken Wasu Manyan Sarakuna 2 Kan Rikicin Kabilanci

Kogi: Ana Binciken Wasu Manyan Sarakuna 2 Kan Rikicin Kabilanci

210
0

Gwamnatin jihar Kogi, ta ce tana gudanar da bincike a kan wasu manyan sarakunan jihar guda biyu, game da wani mummunan tashin hankalin da ya yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutane 9 tare da kona gidaje da dama a ‘yan kwanakin da su ka gabata a karamar hukumar Bassa.

Rahotanni sun nuna cewa, manyan sarakunan biyu masu daraja ta daya, da sun hada da Sarkin Bassa Alhaji Khalid Ali Bukar Sarkin Mozum, da Chif William Keke, yanzu haka su na hannun hukumomi domin gudanar da bincike a kan lamarin.

Gwamnatin jihar Kogi, ta ce yankin Bassa ya dade ya na fama da tashin hankalin da ya shafi kabilanci da rikicin mallakar filaye a tsakanin ‘yan kabilar Egbira da Bassa Komo.

Kwamishinan labarai na jihar Kogi Mr. Kinsley Fanwo, ya ce an gayyaci Sarakunan ne domin su yi karin haske a kan matsaloli da dama, wadanda za su taimaka wajen dorewar zaman lafiya a karamar hukuma Bassa.

Ya ce gwamnati ta yi kokarin dawo da zaman lafiya a yanki, kuma akwai wani tsari da aka samar da zai hana aukuwar abin da ya faru a baya.

Leave a Reply