Home Labaru Sanata Ahmad Lawan Ya Taya Musulmin Najeriya Murna

Sanata Ahmad Lawan Ya Taya Musulmin Najeriya Murna

12
0

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya taya al’ummar Musulmin Najeriya murnar zagayowar ranar Maulidi a wata sanarwa da ya fitar.

Ahmad Lawan ya ce ranar Maulidi rana ce da ya kamata Musulmi da sauran mabiya wasu addinan su tuna da alfanun zaman lafiya da girmama juna da tsoron Allah kamar yadda Annabi Muhammadu Salallahu Alaihi Wasallam ya koya mana tsawon rayuwar sa.

Ya ce yin hakan na da matukar amfani a yanzu da ake tsananin bukatar waɗannan halaye na sa don kawo waraka a ƙasar mu tare da karfafa danƙon zumunci a matsayin mu na mutane masu imani kuma ƴan Najeriya.

Shugaban majalisar dattawan ya ce gwamnatin Najeriya da Majalisar dokoki za su ci gaba da yin aiki sosai don samar da yanayi mai kyau na zaman lafiya da fahimtar juna da ci gaba Najeriya.

Ya kuma bukaci ,yan Najeriya su ci gaba da addu’a da tallafa wa hukumomin tsaro a koƙarin su na kare lafiya da dukiyoyin al’umma.