Gwamnan jihar Zamfara Mohammed Bello Matawalle, ya bada umarnin a kai ‘yan mata biyar da aka sako daga hannun ‘yan bindiga asibiti, domin a duba lafiyar su na ‘yan kwanaki kafin su koma cikin iyalan su.
A wata sanarwa da mataimaki na musamman ga gwamnan a kan harkokin yada labarai Zailani Bappa ya sanya wa hannu, ya ce maitaimakin shugaban ‘yan sandan Nijeriya mai kula da shiyya ta 10 AIG Bello Sani Deljan, da kwamishin ‘yan sanda na jihar CP Kolo Yusuf ne su ka jagoranci yaran zuwa fadar gwamnati bayan an kubutar da su daga hannun’yan bidigar.
Gwamna Matawalle, ya yaba wa jami’an tsaron da ke aiki a jihar, tare da kiran su kara kaimi wajen kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga da ke addabar jihar Zamfara.
A karshe gwamnan ya yi kira ga al’umar jihar su kai rahoton duk wani mutumin da su ke zargi da tsegunta wa ‘yan bindiga bayanai ga hukumomi.