
Kungiyar Malaman jami’o’i ta Nijeriya ASUU, ta soki gwamnatin tarayya a kan biyan malaman jami’o’i rabin albashin watan Oktoba.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar ya fitar, ya ce kungiyar ta yi Allah wadai da irin biyan da gwamnatin tarayya ta yi wa ‘ya’yan ta.
Sanarwar, ta kuma zargi gwamnatin Tarayya da yunkurin maida malaman jami’a ma’aikatan wucin-gadi, wadanda za su yi aiki a biya su nan take.
Wannan dai ya na zuwa ne, bayan gwamnatin tarayya ta biya malaman rabin albashin watan Oktaba, ta na mai cewa ba za ta biya malaman kudin aikin da ba su yi ba.
You must log in to post a comment.