Home Labaru Kasafi: ‘Yan Sanda Sun Tarwatsa Mutanan Da Suka Raka Gwamna Buni Majalisa

Kasafi: ‘Yan Sanda Sun Tarwatsa Mutanan Da Suka Raka Gwamna Buni Majalisa

266
0

Rundunar yan sandan Nijeriya ta harba barkono mai sa hawaye a dandazon wasu mutane ka suka yi cincirindo a kafar shiga a majalisar dokokin jihar Yobe.

Lamarin dai ya faru ne ne jim kadan bayan gwamnan jihar Mai Mala Buni ya shiga zauren majalisar domin gabata da kasafin kudin shekara ta 2020 a gaban majalisar.

Bayan isowar gwamnan majalisar dai, sai ‘yan sandan su ka gaza dai-dai-ta dandazon mutanan da su ka rako gwamnan, lamarin da ya sa suka harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa dandazon mutanan.