Home Labaru Gwamnan Filato Zai Kashe N100M Wajen Gyara Gidan Sauke Bakin SA

Gwamnan Filato Zai Kashe N100M Wajen Gyara Gidan Sauke Bakin SA

75
0

Gwamnatin jihar Filato, za ta kashe naira miliyan 100 wajen gyara gidan saukar bakin Simon Lalong, yayin da gaba daya ma’aikatar al’adu da yawon bude ido za ta kashe Naira Miliyan 88.

Kwamishanan kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki na jihar Sylvester Wallangko ya bayyana haka, yayin da yak e fashin baki a kan kasafin shekara ta 2022.

Wallangko, ya ce kasafin shekara ta 2022 ba kai yawan na shekara ta 2021 ba, saboda an samu ragin Naira Biliyan 40 daga Naira Biliyan 147 a shekara ta 2021 zuwa Naira Biliyan 106 a shekara ta 2022.

Ya ce an ware wa Ma’aikatar al’adu da yawon bude ido Naira Mliyan 88, sannan za a gina sashen manya a tashar jirgin sama kasa da kasa a kan kudi Naira Miliyan 60, yayin da za a gyara gidan saukar bakin gwamna Lalong a kan Naira Miliyan 100.