Tsohon gwamnan jihar Abia Orji Kalu, ya zargi gwamnonin Nijeriya da yin sakaci har matsalar tsaro ta kai matsayin da ta ke a yau.
Yayin wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na Arise, Orji Kalu ya ce gwamnoni ne su ka fi kusa da mutane, don haka sun san masu aikata ta’addanci a jihohin su.
Ya ce idan gwamnoni za su mike tsaye su yaki matsalar tsaro a johohin su su tashi tsaye, domin shugaba Muhammadu Buhari ya yi iyakar kokarin sa.
Orji Kalu, ya ce shugaba Buhari ba zai je jihohin su ya yi masu yaki da ‘yan ta’adda ba, su ne za su mike tsaye su tabbatar sun yake su.
Ya ce gwamnoni da yawa ba su taka rawar gani ba wajen kawo karshen matsalar tsaro a jihohin su, alhalin sun fi kusa da ‘yan ta’addan amma ba su iya tabuka komai a kai.