Home Labaru Yan Adaidaita Sahu Sun Nemi Afuwar Gwamna Nasir El-Rufa’i A Kaduna

Yan Adaidaita Sahu Sun Nemi Afuwar Gwamna Nasir El-Rufa’i A Kaduna

105
0

Shugabannin kungiyar matuka Keke Napep na jihar Kaduna, sun nemi afuwar Gwamnan jihar Nasir El-Rufa’i bisa laifin da wasu ‘yan kungiyar su ka yi.

Gwamnatin jihar Kaduna dai ta kafa sabuwar dokar takaita hada-hadar Keke Napep daga karfe 6 na safe zuwa 7 na yammacin kowace rana.

Jawabin neman afuwar direbobin kuwa ya na kunshe a cikin wata sanarwa da Shugaban kungiyar Aminu Ibrahim ya fitar a Kaduna.

Aminu Ibrahim, ya kuma roki gwamnati ta saki kekunan adaidaita sahun da jami’an ta su ka kama, ya na mai cewa, sun bada hakurin ne sakamakon saba dokar da wasu ‘yan kungiyar su su ka yi na tuka ababen hawan su don neman abinci.