Home Labaru Gwamnan Bauchi Ya Rushe Shugabannin Riko Na Kananan Hukumomi

Gwamnan Bauchi Ya Rushe Shugabannin Riko Na Kananan Hukumomi

61
0

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad Abdulkadir, ya
rushe dukkan shugabannin riko na kananan hukumomin jihar
nan take.

Matakin dai ya biyo bayan karewar wa’adin mulkin su ne a matsayin shugabannin rikon kwarya.

Sakataren Gwamnatin jihar Bauchi Barista Ibrahim Muhammad Kashim ya bayyana amincewar gwamnan a cikin wata sanarwar da ya raba wa manema labarai a Bauchi.

Sanarwar ta ce, an umarci dukkan shugabannin su mika ragamar tafiyar da harkokin kananan hukumomin su ga manyan jami’an sashen gudanar da mulki na kananan hukumomi har zuwa lokacin da za a nada wasu.

Gwamna Bala Muhammad, ya yi fatan alkairi ga ‘yan kwamitin rikon kwarya na kananan hukumomi masu barin gado, tare da yi masu fatan samun nasarori a rayuwar su ta gaba.

Leave a Reply