Home Labaru Sarakuna Sun Yi Maraba Da Shirin Ba Su Dama Da Majalisar Wakilai...

Sarakuna Sun Yi Maraba Da Shirin Ba Su Dama Da Majalisar Wakilai Ta Yi

106
0

Sarakunan gargajiya a karkashin Jagorancin kungiyar
sarakunan wanzar da zaman lafiya, sun yi maraba da shirin
majalisar wakilai na ba su damar bada gudunmawa a cikin
kundin tsarin mulkin Nijeriya.

Idan dai ba a manta ba, kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas ya shelanta cewa, majalisar za ta yi aiki domin tabbatar da ganin ta ba sarakunan damar bada gudunmawa a cikin kundin tsarin mulki.

Tajudeen Abbas ya bayyana hakan ne, yayin wata ziyara da ya kai fadar mai martaba Sarkin Zazzau Ahmed Nuhu Bamalli.

A cikin wata sanarwar da shugaban kungiyar na kasa Eze- Igwe William Ezugwu ya fitar a madadin sauran sarakunan, sun bayyana yunkurin majalisar a matsayin abin yabawa, inda su ka ce sarakuna su na da gudunmawar da za su iya badawa a kudin tsarin mulki, musamman a bangaren wanzar da zaman lafiya da rage kalubalen rashin tsaro a Nijeriya.

Sarakunan sun kara da cewa, yunkurin zai zama tamkar kafa tirihi ga majalisar ta 10, musamman domin wanzar da zaman
lafiya a fadin kasar nan.

Leave a Reply