Home Labaru Jami’an Kwastam Sun Kama Manyan Makamai Da Alburusai A Legas

Jami’an Kwastam Sun Kama Manyan Makamai Da Alburusai A Legas

244
0

Hukumar hana fasa-kwauri ta Nijeriya, ta ce ta kama
jakunkuna dauke da manyan makamai da alburusai a birnin
Legas.

Bayanin hakan, ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Hukumar ta wallafa a shafukan ta na sada zumunta.

Sanarwar, wadda kakakin hukumar ya sanya wa hannu, ta ce hukumar ta kama bindigogi talatin da daya da alburusai da aka boye a wasu duro-duro da buhunnan gawayi a makonni biyu na watan Yulin shekara ta 2023.

Haka kuma, hukumar ta ce ta kama mutane biyu da ake zargi hannu da lamarin.

Sanarwar ta ambato shugaban riko na hukumar Bashir Adewale Adeniyi ya na cewa, sashen leken asiri na hukumar ya hada gwiwa da rundunar ‘yan sanda da jami’an hukumar DSS da na hukumar hana sha da fataucin kwaya NDLEA wajen yin kamen.

Leave a Reply