Home Labaru Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Bindiga A Dazuzzukan Sokoto Da Katsina

Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Bindiga A Dazuzzukan Sokoto Da Katsina

13
0

Dakarun Sojin Nijeriya sun yi nasarar hallaka ‘yan bindiga da dama, tare da lalata maɓoyar su a dazuzzukan jihohin Sokoto da Katsina.

A jihar Sokoto, sojojin sun kai hare-hare ne ta sama a dazuzzukan Mashema da Yanfako da Gebe da Gatawa a ƙananan hukumomin Isa da Sabon Birni.

Wata majiyar soji ta sheda wa manema labarai cewa, an samu nasarar hakan ne sakamakon ruwan boma-boman da su ka yi, bayan an gano wuraren da ‘yan ta’addan su ke buya.

A jihar Katsina kuwa, majiyar ta ce jiragen yaƙin sama sun yi ruwan boma-bomai a maɓoyar ‘yan ta’addan da ke dajin Rugu, wanda ke iyaka da Kananan Hukumomin Safana da Danmusa da Kankara.

Yayin wadannan hare-hare, an lalata sansanin wani ɗan ta’adda mai suna Gajere, inda aka kashe yaran sa 34, sannan akalla wasu 20 sun samu raunuka.