Home Labaru Gwamna Zulum Ya Tallafawa Sojojin Da Suka Samu Rauni Da Kudade

Gwamna Zulum Ya Tallafawa Sojojin Da Suka Samu Rauni Da Kudade

43
0

Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno ya ziyarci sojojin da suka jikkata a fafatawar da mayaƙan Boko Haram a garin Rann na jihar.

Da yake tattaunawa da su a Asibitin Maimalari Barracks, gwamnan ya bayar da umarnin ba su kyautar naira miliyan biyar, inda za a ba su da kuma sauran waɗanda ke kwance a asibitin ko da kuwa ba su da alaƙa da fafatawar ta Rann.

Wata sanarwa daga fadar gwamnatin jihar ta ce Kwamandan Bataliya ta 7, Birgediya Janar Abdulwahab Eyitayo, ne ya tarɓi Gwamna Zulum.

A ranar Juma’a da ta gabata ne mayaƙan ƙungiyar ISWAP da na Boko Haram suka kai wa sansanin sojan Najeriya hari a garin Rann na Ƙaramar Hukumar Kala Balge da ke kan iyakar ƙasar nan da Kamaru.

Wata sanarwa da rundunar sojan ta fitar ta ce dakarunta sun kashe gomman ‘yan bindigar tare da ƙwace makamansu. Sai dai soja bakwai sun rasu a gumurzun.