Home Labaru Gobara Ta Hallaka Mutum 38 A Gidan Yarin Burundi

Gobara Ta Hallaka Mutum 38 A Gidan Yarin Burundi

196
0

A ƙalla mutum 36 ne suka mutu wasu da dama kuma suka jikkata sakamakon wata gobara da ta tashi a gidan yarin kasar Burundi.

Mataimakin shugaban ƙasa Prosper Bazombanza ya shaida wa manema labarai cewa gobarar ta tashi ne a wani gidan yari mai cunkoso dake Gitega babban birnin ƙasar, inda a ƙalla mutum 69 suka jikkata.

Hotunan da aka yaɗa a shafukan intanet sun nuna yadda ginin gidan ke ci da wuta tare da wasu tarin gawarwakin fursunoni.

Wani Fursuna da ya zanta da kafar yada labarai ta BBC ya bayyana lamarin a matsayin wani babban bala’I, inda yace kusan kashi 90 cikin 100 na ɗakunan kwana sun ƙone ƙurmus.

Shima wani ɗan jarida da ya shaida aukuwar lamarin ya fadawa BBC cewa ma’aikatan jinya daga asibitin Gitega sun shiga gidan yarin domin taimaka wa waɗanda lamarin ya rutsa da su.

Rahotanni sunce Gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 4 na yamma agogon ƙasar, daidai da ƙarfe 2 agogon GMT.

Wani saƙon tuwita da ministan harkokin cikin gida na Burundi ya wallafa ya cewa matsalar wutar lantarki ne ta jawo tashin gobarar.

Ko a watan Agusta ma an yi wata gobarar a gidan yarin, inda mahukunta suka ɗora alhaki a kan wutar lantarki. Sai dai a wancan lokacin gobarar ba ta jawo asarar rayuka ba.

Leave a Reply