Home Labaru Gwamna Matawalle Ya Rike Min Kudin Fansho Da Alawus – Abdulaziz Yari

Gwamna Matawalle Ya Rike Min Kudin Fansho Da Alawus – Abdulaziz Yari

184
0
Abdulaziz Yari, Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara
Abdulaziz Yari, Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara

Tsohon gwamnan jihar Zamfara AbdulAziz Yari, ya ce gwamna Bello Matawalle ya hana shi kudin fansho da wasu hakkokin sa a matsayin tsohon gwamna kamar yadda dokar jihar ta tanada.

A cikin wata wasika da ya aike wa Matawalle, Abdulaziz Yari ya bukaci gwamnan ya biya shi kudaden saboda babu wani dalilin da zai sa ya rike ma shi kudi.

Ya ce tun da ya sauka mulki, sau biyu kacal aka biya shi kudin kula da kan sa naira miliyan 10 a wata, ya na mai cewa, dokar jihar ta tanadi a ba tsofaffin gwamnoni da mataimakan su, da tsofaffin shugabannin majalisar jihar da mataimakan su, alawus a kowane wata.

A cewar sa, ya na son jawo hankalin Matawalle a kan wannan doka da aka gyara, wadda ta yi tanadin cewa daga cikin abubuwan da tsohon gwamna ya cancanci a ba shi shi ne naira miliyan goma a matsayin alawus duk wata, da kuma fansho na daidai kudin albashin da ya ke dauka lokacin da ya ke kan mulki.