Home Labaru Gwamna Ganduje Ya Kafa Sabon Sharaɗi Ga ‘Yan Takara A Jihar Kano

Gwamna Ganduje Ya Kafa Sabon Sharaɗi Ga ‘Yan Takara A Jihar Kano

13
0

Gwamnatin jihar Kano, ta ce duk dan jam’iyyar APC da ke neman wani mukamin jam’iyya sai ya yi gwajin shan miyagun kwayoyi.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Muhammad Garba ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya shawarci dukkan ‘yan takara su je ofishin hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA.

Muhammad Garba, ya ce sai da aka gudanar da makamancin wannan gwajin ga ‘yan takara a zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi.

Ya ce tuni gwamna Ganduje na jihar Kano ya sanar da hukumar NDLEA ta gudanar da gwajin, tare da gargaɗin cewa gwamnati za ta ɗauki mataki a kan duk wanda ta gano ya na mu’amala da haramtattun kwayoyi.