Home Labaru Yadda Tsofaffin Wasu ‘Yan Nijeriya Su Ka Dankare Biliyoyi A Waje

Yadda Tsofaffin Wasu ‘Yan Nijeriya Su Ka Dankare Biliyoyi A Waje

23
0

Nijeriya na daga cikin kasashen da ake fama da matsananciyar fatara a Duniya, inda Alkaluma su ka nuna kashi 90 cikin 100 na al’ummar wasu jihohi ba su samun ko da Dala1 a rana, amma duk da haka akwai tsirarrun da su ka mallaki biliyoyin kudi.

Wata majiya ta ce, bayanan da aka samu daga fallasar Pandora Papers, sun nuna akwai wasu manya da su ka boye tarin dukiyoyi a kasashen waje.

Bincike ya nuna cewa, shugabanni da jami’an gwamnati da attajirai da dama daga kasashe akalla 91 sun tara tulin dukiyoyin da su ke juya wa a boye.

Daga cikin wadanda aka samu a Nijeriya, akwai tsofaffin gwamnonin mulkin soja da wani tsohon soja da hadimin tsohon shugaban kasa da wasu ‘yan kasuwa da attajirai.