Home Labaru Gwamna El-rufai Ya Yi Nasara A Kan Jaridar Da Ta Yi Masa...

Gwamna El-rufai Ya Yi Nasara A Kan Jaridar Da Ta Yi Masa Karya A Kotu

62
0

Babbar Kotun Shari’a da ke Kaduna, ta yanke wa kamfanin jaridar Today hukuncin ta biya gwamna El-Rufa’i naira miliyan 10 a matsayin diyyar ƙazafin da ta yi ma shi.

A shekara ta 2015 dai, Jaridar ta buga labarin cewa El-Rufa’i ya bayyana makudan kuɗi har naira biliyan 90 da wasu kantama-kantaman gidaje 40 a matsayin kadarorin da ya mallaka kafin ya zama gwamna.

Bayan buga wannan labari ne El-Rufai ya garzaya kotu, inda ya  ƙalubalanci labarin da cewa ƙazafi aka yi ma shi, amma bai bayyana abin da jaridar ta wallafa ya mallaka ba.

Alkalin Kotun mai shari’a M.L Mohammed, ya ce bayan nazari da binciken da kotu ta yi da kuma sauraren dukkan ɓangarorin, ta gano cewa an yi wa El-Rufai karya ne da kuma yi ma shi kazafi na babu gaira babu dalili.

Tuni dai kotun ta yanke hukuncin cewa, Kamfanin jaridar zai biya El-Rufai diyyar naira miliyan 10, sannan ta nemi yafiyar gwamnan, tare da alkawarin ba za ta sake aikata irin haka ba.