Home Labaru Gwamnatin Tarayya Ta Karbi Bashin N8.29 Trillion Cikin Kudin Yan Fansho

Gwamnatin Tarayya Ta Karbi Bashin N8.29 Trillion Cikin Kudin Yan Fansho

22
0

Gwamnatin tarayya ta karbi bashin Naira Tiriliyan 8 da Biliyan 29 daga cikin kudin .yan fansho da ke ajiye zuwa watan Agusta na shekara ta 2021.

Rahotanni sun Ambato wata majiya na cewa, duk da rashin amincewar da mutane su ka nuna a kan wannan niyyar a baya, amma gwamnati ta bi ta bayan fage da sunan zuba jari wajen karbar kudaden.

Idan dai za a iya tunawa, a shekara ta 2019, majalisar tattalin arzikin Nijeriya ta bukaci karbar bashin Naira Tiriliyan 2 daga kudin fansho domin gudanar da wasu manyan ayyuka.

A baya dai an ruwaito shirin gwamnatin tarayya na aron kudaden ‘yan Nijeriyan da ke asusun da aka dade ba a waiwaya ba, da kuma kudaden masu hannun jarin da aka dade ba a bibiya ba.